Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Sheikh Naeem Qasim, babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Labanon, ya bayyana a yau (Asabar) a wani jawabi kan bikin Idin aiko Manzon Allah (SAW): Annabci shine hanyar cimma kyawawan halaye na ɗabi'a da ingantacciyar rayuwa ga ɗan adam.
Da yake mayar da martani kan abubuwan da suka faru a baya-bayan nan a yankin Yammacin Asiya, Sakatare Janar na Hizbullah na Lebanon ya ce: "Trump na neman tsoma baki a dukkan sassan duniya da kuma sarrafa kasashe domin kwace kadarori, kayan aiki da man fetur da hana gudanar Rayuwar dimokuradiyya, Musulunci da 'yanci".
Da yake ishara da fitinar Amurkawa da sahyoniya a Iran, Naeem Qasim ya ce: "Makiya suna kokarin raunana Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta hanyar haifar da hargitsi da tashin hankali bisa taimakon sojojin haya na Mossad da na Amurka, amma miliyoyin Iraniyawa sun fito kan tituna wanda a fitowar farko mutane maza da mata miliyan uku a Tehran".
Ya kara da cewa: "'Yan haya na Mossad da Amurka sun yi amfani da zanga-zangar lumana ta jama'a na adawa da yanayin tattalin arziki wajen haifar da hargitsi da tashin hankali, amma duk da goyon baya da tsokanar da aka yi bisa jagorancin Trump, ba za su iya canza fuskar Iran ba".
Ya ci gaba da cewa: “Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kasance kasa mai cin gashin kanta tun daga shekarar 1979 wacce ta dogara da iyawar da kwarewar al’ummarta kuma ta goyi bayan Gwagwarmaya mai inganci, musamman gwagwarmaya kan gwamnatin Isra’ila masu mamaye, sun shafe fiye da shekaru 46 suna kokarin raunana Jamhuriyar Musulunci.
Amma tare da hikimar jagoranta, sun sami damar dakile tsare-tsaren Amurka, mun tsaya tsayin daka tare da Iran, jama'a, jagoranta da juyin juya halinta, kuma mun ɗauke shi a matsayin mai ƙarfi da jajircewa.
Ya jaddada: "Amurka ba ta son tsarin 'yanci, saidai tana neman sarrafa jama'a, zaɓin su da iyawarsu, da kuma tallafawa abokan gaba na Isra'ila don faɗaɗa tasirinta a yankin". Sakatare Janar na kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, ya yi nuni da cewa, zanga-zangar da aka yi a Iran ta bayyana bukatun jama'a, ya ce: "Mun tsaya tare da al'ummar Iran, jagoran juyin juya hali kuma muna ganinsa a matabbaci da karfi.
Venezuela, laifin karni ya faru ne tare da sace shugabanta, suna neman albarkatun Venezuela da man fetur kuma suna ƙoƙarin kai shi zuwa Amurka." Trump yana son albarkatun Venezuela da mai kuma yana son ya haɗe ta da Amurka.
Naeem Qasim ya kara da cewa: "Trump bai wadata da Venezuela ba, sai dai ma yana don kwace Greenland, Cuba, Kanada da Tarayyar Turai, duk ayyukansa yana yin su ne da nufin sarrafawa".
Shugaban Hezbollah a Lebanon kuma ya yi kira da a gudanar da wani yunkuri na duniya a matakin kasashe da su shaida wa Amurka cewa ya Isa Hakanan.
Your Comment